Bangaren kasa da kasa; An baje kolin wasu daga cikin littfana addinin musulunci a kasuwar baje kolin liffai ta kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Japan, daga cikin littafan akwai na sanin akidojin addinin musulunci da al'adunsa, da kuma kur'ani mai tsarki, wannan dai shi ne karo na goma sha shida da ake gudanar da baje kolin littfai a Japan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Saudiyya ta Riyad cewa; An baje kolin wasu daga cikin littfana addinin musulunci a kasuwar baje kolin liffai ta kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Japan, daga cikin littafan akwai na sanin akidojin addinin musulunci da al'adunsa, da kuma kur'ani mai tsarki, wannan dai shi ne karo na goma sha shida da ake gudanar da baje kolin littfai a Japan. Bayanin ya ci gaba da cewa sama da cibiyoyin buga tare da yada littafai 500 suke halartar taron baje kolin littafan na kasa da kasa a kasar Japan, wadanda suka fito daga kasashe 30 na duniya, daga ciki kuwa hard a kasashen musulmi.
432014