Bangaren kasa da kasa; An gudanar da taron girmama mahardata kur'ani maitsarki da suka samu nasara a gasar hardar kur'ani da aka gudanar a kasar Hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Dubai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran wam cewa; An gudanar da taron girmama mahardata kur'ani maitsarki da suka samu nasara a gasar hardar kur'ani da aka gudanar a kasar Hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a birnin Dubai. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gasar ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa tsakanain cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da kuma kungiyoyin musulmi na kasar faransa, gami da hadin gwiwa da kwalejin nazari da bincike kan ilimin sanin halayyar dan adam a kasashen turai. Mutane 160 suka shiga cikin gasar da suka hada maza da mata, dukkaninsu kuma musulmi ne mazauna kasar faransa, da suka hada da 'yan asalin kasar da kuma wadanda suka je suna zaune a kasar.
431888