Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a birnin New York na kasar Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a cikin watan Ramadan mai zuwa, a babban ginin cibiyar kula da harkokin addini ta mabiya mazhabar shi'a da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na sijni a shafinsa na internet cewa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai tsarki a birnin New York na kasar Amurka, wanda aka shirya gudanarwa a cikin watan Ramadan mai zuwa, a babban ginin cibiyar kula da harkokin addini ta mabiya mazhabar shi'a da ke birnin. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gasar ne karkashin wani shiri na hadin gwiwa tsakanain cibiyar kula da harkokin gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da kuma kungiyoyin musulmi na kasar faransa, gami da hadin gwiwa da kwalejin nazari da bincike kan ilimin sanin halayyar dan adam a kasashen turai. Mutane 160 suka shiga cikin gasar da suka hada maza da mata, dukkaninsu kuma musulmi ne mazauna kasar faransa, da suka hada da 'yan asalin kasar da kuma wadanda suka je suna zaune a kasar.
431982