Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani da ta kebanci watan Ramadan mai alfarma a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar musulunci ta mabiya mazhabar shi'a ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dilalncin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Dubai jama'at cewa; Za a gudanar da gasar karatun kur'ani da ta kebanci watan Ramadan mai alfarma a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar daular larabawa, wanda cibiyar musulunci ta mabiya mazhabar shi'a ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar gudanar da wannan gasa ita ce karfafa gwiwar matasa wajen mayar da hankali kan karatu da harder kur'ani mai tsarki, da kuma sanin hakikanin furuci da kalmomin kur'ani kamar yadda suke, wato limin tajwidi. Za a kasa gasar zuwa kashi biyu, kashi na farko bangaren mata ne, daga bisani kuma bayan kamamla bangaren mata za a shiga bangaren maza. Za a gudanar da gasar a dukkanin dararen watan Ramadan.
432419