Bangaren kasa da kasa; An sayar da wani kur'ani maid a aka danganta tarihinsa da karni na bakwai hijira kamariyya a birnin London na kasar Birtaniya a kan zunzurutun kudi har fan miliyan biyu da rabi, wato sama da yuro miliyan dari uku kenan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran infosoir cewa; An sayar da wani kur'ani maid a aka danganta tarihinsa da karni na bakwai hijira kamariyya a birnin London na kasar Birtaniya a kan zunzurutun kudi har fan miliyan biyu da rabi, wato sama da yuro miliyan dari uku kenan.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shi ne karon farko da aka sayar da wani littafi da irin wannan tsada. A wasu lokuta da suka gabata an sayar da wani dutse da aka rubuta wasu kalmomi a kansa da suke komawa zuwa ga musulunci a kasar pain, wanda aka sayr da shi a lokacin akan tsabar kudi har fan miliyan daya da dubu dari uku.
432539