IQNA

Kisan 'Yar Masar Jamus Na Nuni Da Karuwar Kyamar Musulunci A Turai

15:44 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802160
Bangaren kasa da kasa; Kisan gillan da aka yi marwa sharbini 'yar kasar masar a kasar Jamus saboda saka hijabin musulunci, yana nuni ne da yadda kyamar addinin musulunci ke ci gaba da karuwa a cikin kasashen nahiyar turai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Akhbar yaum ta kasar masar cewa; minister mai kula da harkokin addinin musulunci na kasar Masar ya bayyana cewa; Kisan gillan da aka yi marwa sharbini 'yar kasar masar a kasar Jamus saboda saka hijabin musulunci, yana nuni ne da yadda kyamar addinin musulunci ke ci gaba da karuwa a cikin kasashen nahiyar turai. Bayanin ya ci gaba da cewa daruruwan daliban jami'a ne suka taru jiya a birnin Alkahira domin yin Allawadai da wannan mummunan aiki, tare da kiran gwamnatin kasar Jamus da ta dauki dukkanin matakai na tabbatar da kare rayukan mabiya addinin masulunci da ke zaune a kasar.

433152



captcha