Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga reshen watsa labaransa na birnin Qom cewa; Babban malamain addinin musulunci a kasar Iran Ayatollah Nuri hamidani ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya soki lamirin masu kare hakkin bil adama a duniya bayan da suka yi gum da bakinsu dangane da kisan da ake yi wa mabiya addinin musulunci a kasar China. Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin bayanin na babban malamin ya bayyana matakin da masu kare hakkin dan adam suka dauka kan batun kisan kiyashi da danne hakkokin musulmi a kasar China da cewa wannan ya nuna cewa bas u dauki musulmi mutum mai hakki da za a kare ba, wanda kuma hakan ya tabbatar da cewa akwai bangaranci a cikin lamariin nasu.
433250