IQNA

Kasashe 52 Ne Za Su Halarci Gasar Karatun Kur'ani A Iran

15:43 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802164
Bangaren kasa da kasa; Minista mai kula da harkokin addini na kasar Iran ya bayyana a wani zaman taron manema labarai a birnin Tehran cewa; za a gudanar da gasar kur'ani ta kasa da kasa birnin Tehran kamar yadda aka saba a lokutan baya, kuma kasashe hamsin da biyu za su halarci gasar daga sassa daban-daban na duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Minista mai kula da harkokin addini na kasar Iran ya bayyana a wani zaman taron manema labarai a birnin Tehran cewa; za a gudanar da gasar kur'ani ta kasa da kasa birnin Tehran kamar yadda aka saba a lokutan baya, kuma kasashe hamsin da biyu za su halarci gasar daga sassa daban-daban na duniya. Ya ci gaba da taron gasar zai samu halartar makaranta da kuma mahardata. Ya ce bisa la'akari da cewa wannan karon gasar za ta dauki wani sabon salon ta fuskacin inganci, hakan ya sanya an rage yawan kasashen da suke halartar gasar, da kuma adadin masu shiga gasar. Haka nan kuma za a mayar da hankali wajen batun harda daga farkon kur'ani zuwa karshensa.

433170
captcha