Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro na wayar da kan yara 'yan makaranta dangane da addinin musulunci da kuma koyarwarsa, da kuma sanin yadda ya kamata su rayu a cikin rayuwarsu ta zamnatakewa a bisa ka'idoji da dokoki na addinin musulunci da tarbiyarsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Peninsula cewa; Za a gudanar da wani zaman taro na wayar da kan yara 'yan makaranta dangane da addinin musulunci da kuma koyarwarsa, da kuma sanin yadda ya kamata su rayu a cikin rayuwarsu ta zamnatakewa a bisa ka'idoji da dokoki na addinin musulunci da tarbiyarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa a taron za a gabatar da laccoci ga yara dangane da koyarwa da tarbiyar addinin musulunci, haka nan kuma taron zai samu halartar yara matasa daga sassa daban-daban na kasar, inda masana musamman ma malaman jami'a da malaman addinin musulunci za su gabatar da bayanai ga taron.
433133