IQNA

Masana Sun Yi Gargadi Dangane Da Karuwar Kyamar Musulmi A Turai

15:41 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802507
Bangaren kasa da kasa; Kimanin masana 92 daga sassa daban-daban na duniya suka fitar da wani bayani na bai daya dangane da hadarin da ke tattare da karuwar kyamar mabiya addinin musulunci a cikin kasashen nahiyar turai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Shark alausat cewa; Kimanin masana 92 daga sassa daban-daban na duniya suka fitar da wani bayani na bai daya dangane da hadarin da ke tattare da karuwar kyamar mabiya addinin musulunci a cikin kasashen nahiyar turai. wanda hakan ke nuni da danne hakkokin musulmi wadanda sun e marassa rinjaye a cikin wadannan kasashen. Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda suka fitar da bayanin sun hadu kan cewa abin da yake faruwa na kyamar mabiya addinin musulunci a nahiyar turai yana tattare da gagarumin hadari, domin kuwa abin day a fara faruwa yanzu a kasar Jamus ya isa ya tabbatar da irin wannan hari, saboda haka suka yi kira da a kara karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban na duniya.

433843


captcha