IQNA

An Bude Wata Cibiyar Musulunci A Birnin Wikeham Na Kasar Birtaniya

15:40 - July 15, 2009
Lambar Labari: 1802511
Bangaren kasa da kasa; An bude wata cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a birnin Wikeham na kasar Birtaniya, da nufin kula da lamurran musulmin kasar da ke zaune a birnin.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Buck Free Press cewa; An bude wata cibiyar kula da harkokin addinin musulunci a birnin Wikeham na kasar Birtaniya, da nufin kula da lamurran musulmin kasar da ke zaune a birnin. Shugaban kungiyar musulmi a birnin Wikeham Ra'uf Shafi ya bayyana cewa babbar manufar bude wannan cibiya dai ita ce karfafa musulmin wannan birnin ta fuskacin dogaro da kansu, da kuma samun wata babbar cibiya da za su rika gudanar da harkokinsu na addini a cikinta, wannan ne ma ya sanya cibiyar ta kunshi bangaren karatu da kuma bangaren ibada, wato azuzuwa na karatu da kuma bababn dakin karatu gami da babban masallaci. Kuma wannnan cibiya za ta iya daukar dubban mutane a lokacin gudanar da tarukan addini.

433785





captcha