IQNA

Shugaban kasar Rasha Zai Kai Ziyara A Babban Masallacin Moscow

22:46 - July 17, 2009
Lambar Labari: 1802688
Bangaren kasa da kasa; Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev zai kai ziyara a babban masallacin birnin Moscow fadar mulkin kasar, inda zai duba aikin ginin masallacin.
Kamfanin dilalncin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Shugaban kasar Rasha Dmitry Medvedev zai kai ziyara a babban masallacin birnin Moscow fadar mulkin kasar, inda zai duba aikin ginin masallacin. Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin wannan ziyara da shugaban kasar ta Rasha zai kai yau a babban masallacin na Moscow da a halin yanzu a ke ci gaba da gininsa, zai gana da shugabannin musulmi, tare da neman Karin bayani daga gare su kan ci gaban da aka samu ta fuskacin ginin masallacin, wanda idan aka kammala gininsa zai zama masallaci mafi girma a duk fadin kasar Rasha.

434368



captcha