IQNA

An Saka Wa Ranar 3 Ga Watan Sha'aban Suna Ranar Karbala

22:45 - July 17, 2009
Lambar Labari: 1802690
Bangaren kasa da kasa; Gwamnan lardin Karbala Amaluddini Majid ya bayyana cewa ranar 3 ga watan sha'aban rana mai albarka, wadda ita ce ranar haihuwar Imam Hussain AS, a kan haka daga wannan shekara an saka wa wannan rana suna ranar Karbala.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na sautul irak cewa; Gwamnan lardin Karbala Amaluddini Majid ya bayyana cewa ranar 3 ga watan sha'aban rana mai albarka, wadda ita ce ranar haihuwar Imam Hussain AS, a kan haka daga wannan shekara an saka wa wannan rana suna ranar Karbala.Ya ci gaba domin raya wannan rana mai albarka, za a ci gaba da gudanar da bukukuwa na tunawa da ranar haihuwar Imam Hussain a birnin Karbala mai alfarma, inda musulmi za su taru domin gabatar da wakoki na yabon manzon Allah da iyalan gidansa da kuma gabatar da rubutattun kasidu gami da sauran kayan fasaha na addini, kamar zane-zane da ke tunarta da mai kallonsu iyalan gidan manzon allah.

434431








captcha