IQNA

Za A Gudanar Da Wani zaman Taro Na Mata Muslmi A Amurka

22:44 - July 17, 2009
Lambar Labari: 1802693
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin New Ark na jahar Calfornia a kasar Amurka, wanda zai kebanci mata musulmi.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na kafar yada labarai ta Event cewa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin New Ark na jahar Calfornia a kasar Amurka, wanda zai kebanci mata musulmi, da nufin kara karfafa musu gwiwa wajen mikewa tsaye domin shiga cikin harkoki na zamantakewa, tare da wayen kansu kan irin rawar da za su iya taimakawa a cikin al'umma ta kowace fuska. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar dai za ta hada matasa daga 'yan shekaru 6 har zuwa 'yan shekaru 18, wadanda za su gabatar da karatun kur'ani. Wasu daga cikinsu za su gabatar da karatun nasu ne a bangaren farko na kur'ani wasu kuma daga kasa zuwa rabin kur'ani wasu kuma za su gabatar da karatun ne daga sama zuwa kasa.

434426



captcha