Bangaren kasa da kasa; Babban malamin addinin nan na kasar labanan Allah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah ya kirayi dukkanin musulmin duniya da su farka daga dogon barcin da suka shiga.
Kamfanin dillancin labaran ikna reshen kasar labanan ya habarta cewa; Babban malamin addinin nan na kasar labanan Allah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah ya kirayi dukkanin musulmin duniya da su farka daga dogon barcin da suka shiga, dangane da makircin da kasashen yammacin turai ke kulla wa addinin musulunci da musulmi a fadin duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa Allamah Fadlollah ya bayyana cewa babban abin da ya ba kasashe masu girman damar kulla makirce-makircensu akn musulmi shi ne barcin da musulmin suka shiga, da rarrabuwar kawuna, wanda dole ne al'ummar musulmi ta kawo karshen hakan.
435225