Bangaren siyasa da zamantakewa; Ayatollah Qabalan mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan ya gana da shugaban majalisar 'yan shia na kasar Bahrain a birnin Beirut.
Kamfanin dillancin labaran ikna reshen birinin Beiruy na kasar Labanan ya habarta cewa; Ayatollah Qabalan mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na kasar Labanan ya gana da shugaban majalisar 'yan shia na kasar Bahrain a birnin Beirut. Bayanin ya ci gaba da cewa; a yayin ganawar tasu sun tabo muhimman batutuwa da suka shafi shirye-shiryen da mabiya mazhabar shi'a suke da su a kasar Bahrain, inda mabiya mazhabar shi'a sun e suke da rinjaye a kasar ta fuskacin yawan jama'a. Ayatollah Qabalan ya kirayi shugaban majalisar mabiya mazhabar shi'a na Bahrain da su kara himma wajen yawaita shirye-shiryen addinin da za su hada kan dukkanin musulmin kasar, domin a hadu a yi wa addini hidima baki daya.
435227