IQNA

An Gudanar Da Gasar Kur'ani Bagare Na Karshe A Kasar Algeria

17:36 - July 18, 2009
Lambar Labari: 1803491
Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen gasar harder kur'ani ta kasa a kasar Algeria wadda ta kebanci mata zalla, wadda aka gudanar da bangaren karshe na wannan gasa a birnin Algiers fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Alkhabar cewa; An kawo karshen gasar harder kur'ani ta kasa a kasar Algeria wadda ta kebanci mata zalla, wadda aka gudanar da bangaren karshe na wannan gasa a birnin Algiers fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa kwamitin kula da harkokin shirya gasar karatu da harder kur'ani na kasar baki daya ne ya shirya gudanar da wannan gasa, kuma an kammalata a jiya, inda mata mahardata kur'ani daga sassa daban-daban na kasar Algeria suka shiga cikin wannan gasa, daga karshe kuma bayan kamala gasar a jiya an sanar da sunayen wadanda suka yi nasara a bangaren harder kur'ani baki daya, da bangaren rabin kur'ani da kuam rubu'in kur'ani mai tsarki.

435238
captcha