Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen zaman taron da aka gudanar a kasar Turkiya na nazari kan al'adu tsakanin matasa musulmi, wanda aka gudanar a birnin Istanbul na kasar ta Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; An kawo karshen zaman taron da aka gudanar a kasar Turkiya na nazari kan al'adu tsakanin matasa musulmi, wanda aka gudanar a birnin Istanbul na kasar ta Turkiya. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar kula da harkokin matasa da al'adun musulmuci ta kasa da kasa ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan zaman taron, wanda ya hada matasa daga kasashen musulmi daban-daban. Faga cikin muhimman abubuwan da taron ya yi dubi a kansa akwai batun kiyaye al'adun musulunci, musamman ma a cikin lokacin da kasashen yammacin turai ke ta hankoron bata dabi'un matasa musulmi, domin nisantar da su daga koyarwa irin ta addinin musulunci.
435232