Bangaren kasa da kasa; Kungiyar kare hakkokin musulmi ta kasa da kasa ta shirya gudanar da wani zaman taro a birnin Sydney na kasar Austaralia dangane da irin kwarewa da musulmi suka nuna a cikin harkoki da dama a kasashen Australia da kuma Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na muhit cewa; Kungiyar kare hakkokin musulmi ta kasa da kasa ta shirya gudanar da wani zaman taro a birnin Sydney na kasar Austaralia dangane da irin kwarewa da musulmi suka nuna a cikin harkoki da dama a kasashen Australia da kuma Amurka, Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taron wanda za a gudanar a cikin watan Agusta mai kamawa, zai mayar da hankali ne kan irin rawar da musulmi suke takawa wajen raya rayuwar zamantakewar al'ummara cikin kasashen biyu, inda ba a barsu a baya ba wajen shiga cikin dukkanin harkokin na rayuwar zamnatakewar al'umma, kama daga bangaren ayyuka har zuwa bangaren kere-kere da dai sauransu, da kuam kafa kungiyoyin bayar da taimako ga masu karamin karfi.
435216