IQNA

An Kawo Karshen Gasar Hardar Kur'ani A Zirin Gaza

16:40 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1803832
Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen gasar harder kur'ani mai tsarki a yankin zirin Gaza, wadda aka yi lakabi da Al-shafi wadda ta kebanci talibai 'yan makaranta.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dilalncin labaran Palastinu cewa; An kawo karshen gasar harder kur'ani mai tsarki a yankin zirin Gaza, wadda aka yi lakabi da Al-shafi wadda ta kebanci talibai 'yan makaranta. Bayanin ya ci gaba da cewa an fara gudanar da wannan shiri ne a karon farko a zirin Gaza, kuma za a ci gaba da gudanar da shi a kowace shekara, da nufin karfafa yara daliban makaranta kan harkokin karatun kur'ani mai tsarki da kuma hardarsa. Shirin ya samu halartar daruruwan dalibai mahardata kur'ani, wadanda suka kara da juna, kuma daga karshe an bayar kyaututtuka ga wadanda suka zo a mataki na daya da na biyu da kuma mataki na uku.

435640


captcha