IQNA

Za A Gudanar Da Taro Dangane Da Tarihin Manzon Allah SAW A Italia

16:40 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1803836
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin False na kasar Italia dangane da tarihi da sirar manzon Allah SAW, domin yin nazari kan darussan da ke cikin tarihinsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar kasar Bahrain ta Alwaqt cewa; Za a gudanar da wani zaman taro a birnin False na kasar Italia dangane da tarihi da sirar manzon Allah SAW, domin yin nazari kan darussan da ke cikin tarihinsa da kuma yadda ya kamata a fassara addini da abin da ya aikata ko ya umurci a aikata a matsayin ma'aunin gane hakikanin addinin musulunci da koyarwarsa. Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da taron ne a cikin shekara mai zuwa, amma yanzu haka an fara gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka kamata, kuma taron zai samu hamalrtar masana musulmi da wadanda ba musulmi ba, domin yin nazari dangane da sirar manzon Allah SAW.

435523


captcha