IQNA

Za A Gudanar Da Wani Taro Kan Me'iraji A Masallacin Qods

16:39 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1803838
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da taro na musamman kan mi'irajin manzon Allah a cikin masallacin Qods mai alfarma, domin tunawa da ranar da manzon Allah ya yi mi'iraji zuwa birnin Qods, daga na kuma ya yi isra'i zuwa sama.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar World Bulletin cewa; Za a gudanar da taro na musamman kan mi'irajin manzon Allah a cikin masallacin Qods mai alfarma, domin tunawa da ranar da manzon Allah ya yi mi'iraji zuwa birnin Qods, daga na kuma ya yi isra'i zuwa sama. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan ba shi karon farko da ake gudanar da wannan zaman taron ba domin duba irin darussan da ke tattare da me'irajin manzon Allah, da kuma matsayin da masallacin Qods yake da shi a cikin addinin musulunci, sai dai sau da yawa a kan fuskancin matsaloli wajen gudanar da zaman taron, domin sojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sukan dauki tsauraran matakan tsaro domin hana gudanar duk wani taro makamancin hakan.

435432




captcha