IQNA

An Karshen Gasar Hardar Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Kuwait

16:39 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1803839
Bangaren kasa da kasa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya da aka gudanar a kasar Kuwait, wadda ta samu halartar mahardata daga sassa daban-daban na kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Kais ta kasar Kuwait cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya da aka gudanar a kasar Kuwait, wadda ta samu halartar mahardata daga sassa daban-daban na kasar, haka nan kuma makaranta daga sassan kasar su ma ba a bar su a baya ba wajen taka gagarumar rawa a cikin wannan gasa. Bayanin ya ci gaba da cewa an fara gudanar da wannan shiri ne a karon farko a kasar, kuma za a ci gaba da gudanar da shi a kowace shekara, da nufin karfafa yara daliban makaranta kan harkokin karatun kur'ani mai tsarki da kuma hardarsa. Shirin ya samu halartar daruruwan dalibai mahardata kur'ani, wadanda suka kara da juna, kuma daga karshe an bayar kyaututtuka ga wadanda suka zo a mataki na daya da na biyu da kuma mataki na uku.

435426



captcha