IQNA

Ya Kamata A Karfafa Cibiyoyin Musulunci A Kasashen Musulmi

Bangaren al'adu da fasaha; Ministan kula da harkokin addinin musulunci na kasar Syria Abdulsattar Sayyid, ya bayyana cewa ya kamata gwamnatocin kasashen musulmi su mike tsaye wajen agaza wa cibiyoyin musulunci a kasashen duniya musamamn ma wadanda ke kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ma'aikatar yada labarai ta kasar Syria cewa; Ministan kula da harkokin addinin musulunci na kasar Syria Abdulsattar Sayyid, ya bayyana cewa ya kamata gwamnatocin kasashen musulmi su mike tsaye wajen agaza wa cibiyoyin musulunci a kasashen duniya musamamn ma wadanda ke kasashen musulmi. Bayanin ya ci gaba da cewa ministan ya jaddada cewa cibiyoyin musulunci a kasashen duniya suna taka gagarumar rawa wajen yada ilmomin addinin musulunci a kasashen duniya, haka nan kuma cibiyoyin da suke kasashen turai na addinin musulunci suna bukatar karfafa ta musamman daga kasashen musulmi dmin ci gaba da gudanar da ayyukansu na yada addinin musulunci.

436166