IQNA

Zanga-Zanga A Barlin Kan Allah Wadai Da Kisan Marwa

16:34 - July 21, 2009
Lambar Labari: 1804507
Bangaren kasa da kasa; Kungiyoyin musulmi da mambobin kungiyar agaji ta musulmi a Jamus sun gudanar da zanga-zanga a Jamus kan kisan gillar da aka yi wa Marwa .
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta jiyo jaridar Zaman a kasar Turkiya na watsa labarin cewa: bayan yan kwanaki da kisan gillar da aka yi wata mata musulma yar asalin kasar Masar mai sanye da hijabi a kasar Jamus a gaban alkali ,gwamnatin wannan kasa ta hana yada duk wani labari day a shafi wannan danyan aiki na kisan gilla ,matakin day a hargitsa wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama da hukumomi da kungiyoyi na musulmi gudanar da wata gagaramar zanga-zanga a birnin Barlin na kasar ta Jamus domin nuna bacinnransu a fili.

436564
captcha