A ranar farko ta fara wannan gagaramar gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa a babban dakin taron na kasa da kasa da ke nan birnin Tehran ,dakin taron ya sami kansa cikin wani yanayi na ma'anawiya da hadin kai da kuma tarihi na karatun kur'ani kuma wannan shi ne karo na ashirin da shidda da ake gudanar da irin wannan ga a kowace shekara . Kuma an samu mahalarta wannan gasa ta bana daga kasashe da adam na musulmi da kuma hadi da mai masabkin baki Jamhuriyar musulunci ta Iran.Kuma gabanin fara wannan gasa an gabatar da jawabai masu gamsarwa na sannu da zuwa da kuma suka shafiyanayin da sharidodin wannan gasa.
436563