IQNA

An Bude Wani Shafi Na Internet Domin Gudanar Da Bincike Kan Musulunci

10:35 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1804598
Bangaren kasa da kasa; An bude wani shafin internet musamman domin gudanar da bincike ko nazari kan harkoki da suka shafi addinin musulunci, wanda kowa zai iya yin amfani da shi domin sanin abin da ya buya gare shi dangane da addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Sutun cewa; An bude wani shafin internet musamman domin gudanar da bincike ko nazari kan harkoki da suka shafi addinin musulunci, wanda kowa zai iya yin amfani da shi domin sanin abin da ya buya gare shi dangane da addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan shafin internet yana da karfin gaske da kuma matukar muhimmanci ga dukkanin musulmi masu mu'amala da layin sadarwa na internet a sassa daban-daban na duniya. Ya ci gaba da cewa wannan shafi ya sha banban da sauran shafuka da wata kila ake yin amfani da su wajen gudanar da bincike, domin kuwa yafi karfi a kan sauran.

436842




captcha