Bangaren kasa da kasa; Makaranta da mahardata da suke halartar gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a birnin Tehran, sun bayyana matukar gamsuwarsu dangane da yadda alkalan gasar suke gudanar da alkalancinsu a yayin gudanar da gasar karatun kur'ani, ta hanayar yin adalci a tsakanin dukkanin masu halartar gasar.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga banagren yada labarai na kwamitin da ke kula harkokin gasar karatun kur'anin kur'ani a Tehran cewa; Makaranta da mahardata da suke halartar gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a birnin Tehran, sun bayyana matukar gamsuwarsu dangane da yadda alkalan gasar suke gudanar da alkalancinsu a yayin gudanar da gasar karatun kur'ani, ta hanayar yin adalci a tsakanin dukkanin masu halartar gasar. Bayanin ya ci gaba da cewa taron gasar wanda yake samun halartar daruruwan makaranta daga sassa daban-daban na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen musulmi, wadanda suke halartar tarukan gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a sassa daban-daban na duniya.
436729