IQNA

Karatun Kur'ani Tare Da Tunani Kan Ma'anar Ayoyinsa Na Kai Dan Adam Ga Kamala

14:54 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805089
Bangaren kasa da kasa; Karatun kur'ani mai tsarki tare da yin tunani kan ma'anonin da ke tattare a cikin ayoyinsa, na kai dan adam zuwa ga kamala, ta hanyar samun natsuwa da kuma riskar ilmomi na badini da ke tattare da ma'anoninsa.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanindilalncin labaran ikna da daya daga cikin makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Austaralia da ke halartar taron gasar karatun kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran Mir Mukhtar Hussain Wahab ya bayyana cewa; Karatun kur'ani mai tsarki tare da yin tunani kan ma'anonin da ke tattare a cikin ayoyinsa, na kai dan adam zuwa ga kamala, ta hanyar samun natsuwa da kuma riskar ilmomi na badini da ke tattare da ma'anoninsa. Ya ci gaba da cewa kur'ani yana tattare da wani sirri na musamman wanda kuma babu wanda zai iya riskar hakan sai mai karanta shi tare da yin tunani da la'akari da manonin ayoyinsa tsarkaka.
437022
captcha