IQNA

Sheikh Taruti Na Daya Daga Cikin Alkalan Gasar Kur'ani A Tehran

14:48 - July 23, 2009
Lambar Labari: 1805094
Bangaren kasa da kasa; Sheikh Taruti na daya daga cikin alkalan gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda daya daga cikin fitattun alkaalan gasar kur'ani ta kasa da kasa da suka shahara a duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Tehran cewa; Sheikh Taruti na daya daga cikin alkalan gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki da ake gudanarwa a birnin Tehran, wanda daya daga cikin fitattun alkaalan gasar kur'ani ta kasa da kasa da suka shahara a duniya.
Bayanin ya ci gaba da cewa ; Karatun kur'ani mai tsarki tare da yin tunani kan ma'anonin da ke tattare a cikin ayoyinsa, na kai dan adam zuwa ga kamala, ta hanyar samun natsuwa da kuma riskar ilmomi na badini da ke tattare da ma'anoninsa. Ya ci gaba da cewa kur'ani yana tattare da wani sirri na musamman wanda kuma babu wanda zai iya riskar hakan sai mai karanta shi tare da yin tunani da la'akari da manonin ayoyinsa tsarkaka.

437308

captcha