Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kasar Saudiya Was ta watsa rahoton cewa: Salihu Basira ministan Ilimi mai zurfi a kasar Yamen a cikin wani jawabin bude wannan karamar jami'a da ya gabatar ya bayyana cewa; wannan karamar jami'a wani bangare ne na babbar jami'ar ilimi ta birnin San'a babban birnin kasar Yamen.
437979