A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani daya daga cikin mahardata kur'ani da ya halarci gasar karatu dahardar kur'ani mai tsarki dac aka gudanar a birnin Tehran daga kasar Burkina Fasso Ali Zungaran ya bayyana cewa; Gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki na karfafa musulmi wajen yin tunani da hankaltar ayoyin kur'ani mai tsarki, har ma da wadanda ba musulmi matukar dai suna fahimtar abin da ayoyin ke fada. Ya bayyna matukar jin dadinsa dangane da yadda gasar ta wakana da kuma irin yadda masu karatu suka yi kokari wajen yin kwazo a yayin gudaar da gasar.
438090