IQNA

An Samu Ci Gaba Ta Fuskacin Harkokin Kur'ani A Kasashen Duniya

13:46 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806342
Bangaren kasa da kasa; Ana samun ci gaba ta fuskacin gudanar da harkokin karatun kur'ani a kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi.
Yusuf Kuchan daya ne daga cikin mahalrta gasar karatu da hardar kur'ani da aka gudanar a birnin Tehran ta kasa da kasa, a cikin wata zantawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Ikna ya bayyana cewa; Ana samun ci gaba ta fuskacin gudanar da harkokin karatun kur'ani a kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi, wanda hakan yana matukarv tasiri wajen kara yada harkokin addinin musulunci a fadin duniya. Ya bayyna matukar jin dadinsa dangane da yadda gasar ta wakana da kuma irin yadda masu karatu suka yi kokari wajen yin kwazo a yayin gudaar da gasar.

438340
captcha