IQNA

Mahardatan Kur'ani Na Kasar Malazia Sun Halarci Gasar Kur'ani A Iran

13:46 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806345
Bangaren kasa da kasa; mahardata kur'ani daga kasar Malazia da suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran na Iran, sun bukaci da a kara bangarorin gasar, wadda ake gudanarwa a kasar Iran duk shekara,
Daya daga cikin wadanda suka halarci gasar daga malazia Muhammad Ibrahim Abdullah ya bayyana cewa; mahardata kur'ani daga kasar Malazia da suka halarci gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran na Iran, sun bukaci da a kara bangarorin gasar, wadda ake gudanarwa a kasar Iran duk shekara, wanda kuma wannan shi ne karo na 26 da ake gudanar da irin wannan gasa. Ya ci gaba da cewa lokacin da ake gudanar da gasar kurarre ne, saboda haka suna bukatar da akara yawan lokacin ta yadda hakan zai bayar da damar kara wasu bangarori a cikin gasar. 437923



captcha