IQNA

An Fara Gudanar Da Bangaren Karshe Na Gasar Kur'ani A Yeman

13:45 - July 28, 2009
Lambar Labari: 1806346
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da bangaren karshe na gasar kur'ani a kasar Yeman, wadda ta kebanci yara 'yan makaratun gaba da firamare.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sabanet cewa; An fara gudanar da bangaren karshe na gasar kur'ani a kasar Yeman, wadda ta kebanci yara 'yan makaratun gaba da firamare, kuma ana gudanar da gasar ne a matsayi na kasa baki daya a birnin San'a fadar mulkin kasar ta Yeman. Bayanin ya ci gaba da cewa sama da yara 'yan makaranta 500 ne suke halartar taron na hardar kur'ani da hadisan manzon Allah a kasar Yeman, wanda za a kwashe tsawon mako guda ana gudanarwa. Daga cikin wadanda suke halartar gasar akwai yara maza da kuma 'yan mata.

438368

captcha