Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Iba cewa; An gudanar da tarukan maulidin Imam Hussain AS birnin Karbala mai alfarma a tsakanin hubbarorin Imam Hussain da kuma Abul Fadl Abbas, taron da ya samu halartar dubban musulmi mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da ke kasar Iraki da ma wajen kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa an samu halartar mutane a wannantaron maulidi mai albarka, kamar yadda masu rera wakokin yabon iyalan gidan manzon Allah da kuma masu gabatar da jawabai. Da dama daga cikin wadanda suka halarci taron sun nuna farin cikinsu maras misiltuwa.
439433