IQNA

Za A Bai Wa Shugaban Kungiyar OIC Ihsan Auglo Lambar Yabo

15:08 - August 02, 2009
Lambar Labari: 1807712
Bangaren kasa da kasa; Za A Bai shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Ihsan Aiglo wata lambar yabo ta kasa da kasa; wadda bangaren Ilimin tarihi da falsafa na jami'ar Spain ke bayarwa duk bayan shekaru hudu.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Za A Bai shugaban kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC Ihsan Aiglo wata lambar yabo ta kasa da kasa; wadda bangaren Ilimin tarihi da falsafa na jami'ar Spain ke bayarwa duk bayan shekaru hudu. Bayanin ya ci gaba da cewa za a bayar da wannan kyauta ne bisa la'akari da irin rawar da ya taka a cikin 'yan lokutannan wajen kokarin hada kan kan al'ummomi da kuma karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinai, musamman ma mabiya addinain musulunci da kiristanci, domin wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsu.

440037


captcha