Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar alakhbar da ake bugawa a kasar Masar cewa; An girmama mahardata kur'ani mai tsarki da suka rawar gani a kasar Masar a babban dakin gudanar da taruka na jami'ar Alazhar da ke birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar. Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da gasar kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar ta masar a cikin jami'ar alazhar, inda aka bayar da kyaututtuka na musamman ga wadanda suka taka rawar gani, ko kuma suka zo na daya da na biyu da na uku a rukunoninsu. An kasa gasar ne zuwa rukuni uku, da hakan ya hada bangaren harda, sai kuma kira'a da ilimin sanin ka'idojin karatun kur'ani.
440143