Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar kula da harkokin addinin musulunci da al'adu ta Iran da ke birnin Belgrade na kasar Serbia cewa; Za a baje kolin kayayyakin tarihin addinin musulunci da suka hada da wasu hotuna da suke bayyana tarihin musulunci a Iran a kasar Serbia. Bayanin ya ci gaba da cewa idan aka kwatanta da lokutan baya inda da dama daga cikin al'ummomin nahiyar turai suka dauki tsananin gaba da addinin muslunci sakamakon siyasar da wasu kasashe suka dauka ta bayyana addinin musulunci a matsayin addinin tashin hankali, yanzu hakan ya ragu matuka a kasashe da daman a nahiyar.
440234