Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na shafin internet na kamfanin dillancin labaran CIHAN cewa; Hukumar 'yan sanda ta kasar Birtaniya ta fitar da wata doka a kan 'yan sanda mata na kasar, da take lizimta musu saka hijabi kafin shiga a masallatai a kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa hukumar 'yan sanda ta kasar Birtaniya ta dauki wannan matakin ne domin girmama akidar musulmi, domin kuwa masallaci wuri da yake da tsarki a wurin mabiya addinin musulunci, saboda haka ya zama wajibi ga dukkanin mata 'yan sanda na kasar Birtaniya da su kiyaye wannan doka a fadin kasar.
440477