Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Kossobohaber cewa; Babban malamin addinin muslunci kuma mai bayar da fatawa a kasar Bosniya zai kai wata ziyara ta musamman a yankin Kossovo, wadda za ta kwashe tsawon kwanaki hudu a jere, domin ganawa da musulmi yankin da kuma jin irin matsalolin da suke fuskanta. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan dai ita ce ziyara ta farko babban malamin zai kai yankin Kossovo, kuma tuni musulmin yankin Kossovo suka fara shirye-shiryen tarbarsa, domin suna kallonsa a matsayin babban bakonsu da ya cancanci dukkanin girmamawa.
441497