IQNA

Koyar Da Kur'ani A Matsayin Wajibi Na Shari'a Daya Daga Cikin Manufofin Iran

14:56 - August 02, 2009
Lambar Labari: 1808697
Bangaren kasa da kasa; Koyar da kur'ani a matsayin wani wajibi na shari'a na daya daga cikin manufofin juyin juya halin musulunci a Iran.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da daya daga cikin manyan mambobin majalisar shawarar musulunci ta palastinu a Labanan Sheikh Muhammad Namur Ahmad Zagmut ya bayyana cewa; Koyar da kur'ani a matsayin wani wajibi na shari'a na daya daga cikin manufofin juyin juya halin musulunci a Iran, kuma hakan shi ne babban abin day a bayar da dama wajen samun makaranta da mahardata a Iran, tare da saka kur'ania cikin aiki a dukkanin bangarori ba tare da kebancewa ba. Ya ci gaba da cewa abin koyi ne ga dukkanin muslmin duniya da su kalli yadda al'ummar Iran suke yin riko da kur'ani, wanda kuma hakan ne ya bas u izza a duniya baki daya, wanda hakan ke nuni da cewa riko da kur'ani na tattare da samun izza.

441400
captcha