Bangaren kasa da kasa; Rubutun tafsirin kur'ani mai tsarki tare da yin sharhi da ruwayoyin ahlul bait AS a Iran, daya ne daga cikin sakamako na juyin juyin halin musulunci da aka yi kasar tsawon shekaru talatin da suka gabata.
A wata zantawa da ta hada Musa Gosh daya daga cikin shugabannin cibiyar nan ta alkausar akasar turkiya, da ke da babbar cibiya a birnin Istanbul na kasar Turkiya ya bayyana cewa; Rubutun tafsirin kur'ani mai tsarki tare da yin sharhi da ruwayoyin ahlul bait AS a Iran, daya ne daga cikin sakamako na juyin juyin halin musulunci da aka yi kasar tsawon shekaru talatin da suka gabata, wanda kuma hakan zai amfani duniyar musulmi a halin yanzu da kuma zamuna masu zuwa. Ya ci gaba da cewamalaman tafsirin kur'ani a kasar Iran suna yin kokari matuka domin fitar da hakikanin ma'anonin kur'ani, musamman ma ta fuskacin bayyana ayoyin da ma'anoninsu ta hanyar hadisan ahlul bait AS.
441357