Bangaren kasa da kasa; Za a gina wata babbar cibiyar addinin musulunci a birnin Bodast fadar mulkin kasar Poland, bayan da mahukuntan birnin suka amince da takardun neman izini da musulmin birnin suka aike ma majalisar dokokin Bodast da ita kan hakan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran AFP cewa; Za a gina wata babbar cibiyar addinin musulunci a birnin Bodast fadar mulkin kasar Poland, bayan da mahukuntan birnin suka amince da takardun neman izini da musulmin birnin suka aike ma majalisar dokokin Bodast da ita kan hakan. Bayanin ya ci gaba da cewa; wannan karon farko da mahukuntan kasar Poland suka amince da a gina babbar cibiyar addinin muslunci a birnin Bodast, wadda za ta rika kula da harkokin musulmi na birnin da ma sauran biranan kasar, tare da gudanar da taruka da suka danganci a ddinin musulunci, kama daga bayar da horo da kuma gudanar da taruka na ilmantarwa da dai sauransu.
441637