IQNA

Musulmin Holland Sun Bata Shafin Internet Na Masu Sukar Musulunci A Kasar

22:38 - August 03, 2009
Lambar Labari: 1809284
Bangaren kasa da kasa; Musulmin kasar Holland sun bata wasu shafuka na internet na masu kyamar addinin musulunci a kasar, inda suke yin amfani da wadannan shafuka domin bata fuskar addinin musulunci a duniya ta hanyar yanar gizo.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sabah cewa; Musulmin kasar Holland sun bata wasu shafuka na internet na masu kyamar addinin musulunci a kasar, inda suke yin amfani da wadannan shafuka domin bata fuskar addinin musulunci a duniya ta hanyar yanar gizo. Bayanin ya ci gaba da cewa idan aka kwatanta da lokutan baya inda da dama daga cikin al'ummomin nahiyar turai suka dauki tsananin gaba da addinin muslunci sakamakon siyasar da wasu kasashe suka dauka ta bayyana addinin musulunci a matsayin addinin tashin hankali, yanzu hakan ya ragu matuka a kasashe da daman a nahiyar.442629


captcha