IQNA

An Buga Makalolin Da Aka Rubuta Kan Tafsirin Kur'ani A Labanan

16:07 - August 06, 2009
Lambar Labari: 1810243
Bangaren kasa da kasa; An buga tare da yada hadaddun makalolin da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kuma tafsirin ma'anonisa, wanda aka gabatar a kasar Labanan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangarensa na yada labarai a kasar Labanan cewa; An buga tare da yada hadaddun makalolin da aka rubuta kan kur'ani mai tsarki da kuma tafsirin ma'anonisa, wanda aka gabatar a kasar Labanan.
Bayanin ya ci gaba da cewa Kwamitin wanda ya hada kungiyoyi da cibiyoyin addinin musulmunci sama da 40 daga sassa daban-daban na kasashen duniya, zai yi dubi ne a zaman nasa na birnin Tripoli kan muhimman batutuwa da suke ci ma al'ummar musulmi tuwo a kwarya a cikin wannan zamani, da hakan ya hada da cin zarafin da ake yi wa musulmi da mabiya addinin musulunci a wasu kasashe na yammacin turai, tare da daukar matakan da suka dace da nufin kawo karshen hakan.
443328







captcha