IQNA

Indonesia Ta Bukaci Yin Aiki Kafada Da Kafada Tsakanin Musulmi

16:04 - August 06, 2009
Lambar Labari: 1810245
Bangaren siyasa da zamantakewa; Wani kwamitin malaman jami'a da gwamnatin Indonesia ta kafa ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da su yi aiki kafada da kafada.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labaransa na kudancin Asia cewa; Wani kwamitin malaman jami'a da gwamnatin Indonesia ta kafa ya kirayi dukkanin kasashen musulmi da su yi aiki kafada da kafada. Daga cikin muhimman abubuwan da taron ke yin dubin a kansu har da daukar matakai na mayar da martani a ilmance dangane da yadda wasu masana a jami'oin kasashen turai suke kokarin gurbata manufar addinin musulunci a cikin nahiyar turai, wanda hakan na bukatar masana musulmi musamman ma dai malaman jami'oi su mayar da hankali kansa domin kare addinin musulunci daga zagon kasa.
443071



captcha