Bangaren rahoto; An fara gudanar da tarukan da aka saba gudanarwa a cikin watan sha'aban musamman ma daga sha biyar ga wannan wata, da suka hada da tarukan mahdawiyya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren shirya tarukan musulunci na kasar Iran cewa; An fara gudanar da tarukan da aka saba gudanarwa a cikin watan sha'aban musamman ma daga sha biyar ga wannan wata, da suka hada da tarukan mahdawiyya. Babban daraktan cibiyar mahdawiyya mahmud Babbayi ya bayyana cewa jahilci da rashin masaniya na daya daga cikin abin da ke cutar da msulmi, musamman ma bangaren mahdawiyya da mazhabar shi'anci ke shan wahala wajen daidaita tunaninsu