IQNA

An Yi Kakkausar Suka Kan Mai Zanen Batunci Ga Musulunci A Danmark

21:13 - August 09, 2009
Lambar Labari: 1811408
Bangaren kasa da kasa; Musulmin kasar Danmarka sun yi kakakusar suka dangane da aniyar da mai zane-zanen batuncin nan na kasar yake da ita wajen sake yin wani zanen domin yin batunci ga ma'aiki SAW.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na cibiyar kula da harkokin musulmi a kasar Danmark cewa; Musulmin kasar Danmarka sun yi kakakusar suka dangane da aniyar da mai zane-zanen batuncin nan na kasar yake da ita wajen sake yin wani zanen domin yin batunci ga ma'aiki SAW. Bayanin ya ci gaba da cewa mutumin na shirye-shiryen sake watsa wani zanen batunci ga addinin muslunci a cikin 'yan lokutannan, lamarin da ke ci gaba da fuskantar fushin musulmi.

444731
captcha