Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na gidan talabijin din nan na Rasid cewa; An fara gudanar da wani shiri na bayar da horo domin ilmantarwa kan azumin watan Radan a kasar saudiyya, a masallacin Imam Hassan AS da ke garin Saihat a gabacin kasar. Akasarin mazauna wadannan yankunan dai mabiya mazhabar shia ne da suke fuskantar takurawa daga mahukuntan kasar Saudiyya.
445302